26 Satumba 2020 - 15:34
Iran Da Rasha Sun Kara Jaddada Cewa Kokarin Da Amurka Take Yi Na Maida Takunkuman MDD Kan Iran Ba Ya Bisa Ka’ida

Mataimakan ministocin harkokin wajen kasashen Iran da Rasha sun kara jaddada rashin shar’ancin sake maido da takunkuman tattalin arzikin na MDD wadanda aka soke su da kan kasar Iran.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Abbasn Araqchi mataimakin ministan harkokin wajen kasar Iran da kuma tokwaransa na kasar Rasha Sergei Ryabkov suna fadar haka a ganawarsu a safiyar yau Jumma’a.

Jami’an diblomasiyan kasashen biyu har’ila yau sun tattauna batun yarjejeniyar nukliyar kasar Iran JCPOA da yadda kasashen da suke ci gaba da mutunta ta zasu kare ta.

Tun ranar Laraba ce ministan harkokin wajen kasar Iran Mohammad Javad Zareef da tawagarsa suke ziyarar aiki a birnin Mosco babban birnin kasar Rasha.

A makon da ya gabata ne sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya bada sanarwan cewa Amurka ta sake dawo da takunkuman tattalin arzikin da MDD ta dorawa Iran, wadanda kuma aka soke a baya. Ta yi haka ne ita kadai ba tare da amincewa wata kasa a duniya ba.

342/